Sanata Marafa Ya Nuna Alhininsa Game Da Mutuwar Mahaifiyar Dan Majalisa, Mai-Palace.



Muhammad Bashir. 

Tsohon Sanatan Jihar Zamfara ta tsakiya a Majalisar Dattijai ta Najeriya, Sanata Kabiru Garba Marafa, ya jajantawa dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Gusau da Tsafe a zauren majalisar dokoki ta tarayyar Najeriya, Kabiru Amadu Mai-Palace, bisa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Rabi'atu Muhammad, inda ya bayyana ta a matsayin mahaifiya ta gari avar koyi. 

Sanata Marafa wanda ya samu wakilcin wadansu makusantansa, karkashin jagorancin shugaban jam'iyyar APC tsagin Sanata Marafa, Alhaji Surajo Mai-Katako, ya bayyana haka ne yayin da suka kai masa ziyara a gidansa dake Gusau, babban birnin jihar. 

Yayi addu'a Allah ya baiwa dan majalisar hakurin jure rashin da yayi, harma yace rashin bai tsaya ga iyalan dan majalisar ba kawai ba, a'a rashi ne da ya shafi dukkanin al'umar jihar Zamfara. 

A nasa bangaren, dan majalisar ya yabawa Sanata Marafa bisa ziyarar da ya kai masa ta ta'aziyya. 

Dubban al'uma ne dai ke halartar gidan dan majalisar domin taya shi alhinin mutuwar mahaifiyar tasa, tare da yin kyawawan addu'o'i.  

Comments