Sanatan Zamfara Ta Arewa, Sahabi Ya'u Kaiwa Hon. Mai-Palace Ziyarar Ta'aziyya.




Muhammad Bashir.

Sanatan Jihar Zamfara ta arewa a Majalisar Dattijai ta Najeriya, Sanata Sahabi Ya'u, ya jajantawa dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Gusau da Tsafe a zauren majalisar dokoki ta tarayyar Najeriya, Kabiru Amadu Mai-Palace, bisa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Rabi'atu Muhammad, inda ya bayyana ta a matsayin mahaifiya ta gari avar koyi.

Sanata Sahabin dai ya kai ziyarar janatawa dan majalisar bisa rasuwar mahaifiyarka, Hajiya Rabi'atu Muhammad a ranar Asabar 30 ga watan Nuwambar shekarar 2019, tare da wadansu makusantansa a gidansa dake Gusau, babban birnin jihar.

Sanatan yayi addu'a Allah ya baiwa dan majalisar hakurin jure rashin da yayi, harma yace rashin bai tsaya ga iyalan dan majalisar ba kawai ba, a'a rashi ne da ya shafi dukkanin al'umar jihar Zamfara.

A nasa bangaren, dan majalisar ya yabawa Sanata Sahabin bisa ziyarar da ya kai masa ta ta'aziyya.

Dubban al'uma ne dai ke halartar gidan dan majalisar domin taya shi alhinin mutuwar mahaifiyar tasa, tare da yin kyawawan addu'o'i.

Comments